Waƙar Waƙoƙi6hau_bib
1Ina ƙaunataccenki ya tafi,yake mafiya kyau cikin mata?Wace hanya ce ƙaunataccenki ya bi,don mu taimake ki nemansa.2Ƙaunataccena ya gangara zuwa lambunsa,zuwa inda fangulan kayan yaji suke,don yă yi kiwo a cikin lambundon kuma yă tattara furen bi-rana.3Ni na ƙaunataccena ce, ƙaunataccena kuma nawa ne;yana kiwo a cikin furen bi-rana.4Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata, kamar Tirza,kyakkyawa kuma kamar Urushalima,mai daraja kamar mayaƙa da tutoti.5Ki kau da idanu daga gare ni;gama suna rinjayata.Gashinki yana kama da garken awakinda suke gangarawa daga Gileyad.6Haƙoranki suna kama da garken tumakinda suke haurawa daga inda aka yi musu wanka.Kowanne yana tare da ɗan’uwansa;babu waninsu da yake shi kaɗai.7Kumatunki sun yi kamar rummanda aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki.8Sarauniyoyi sittin za su iya kasance a can,da ƙwarƙwarai tamaninda kuma budurwai da suka wuce ƙirge;9amma kurciyata, cikakkiyata, dabam take,tilo kuwa ga mahaifiyarta,’yar lele ga wadda ta haife ta.’Yan mata sun gan ta suka ce da ita mai albarka;sarauniyoyi da ƙwarƙwarai sun yabe ta.10Wace ce wannan da ta bayyana sai ka ce ketowar alfijir?Kyakkyawa kamar wata, mai haske kamar rana,mai daraja kamar taurari a jere?11Na gangara zuwa cikin itatuwan almondon in ga ƙananan itatuwan da suke girma a kwari,don in ga ko inabi sun yi ’ya’yako rumman suna fid da furanni.12Kafin in san wani abu,sha’awarta ta sa ni a cikin keken yaƙin sarkin mutanena.13Ki dawo, ki dawo, ya Bashulammiya;ki dawo, ki dawo, don mu dube ki!ƘaunatacceDon me kuke duban Bashulammiyasai ka ce rawar Mahanayim?