Zabura98hau_bib
Zabura ce.
1Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,gama ya yi abubuwa masu banmamaki;hannunsa na dama da hannunsa mai tsarkisun yi masa aikin ceto.2Ubangiji ya sanar da cetonsaya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai.3Ya tuna da ƙaunarsada kuma amincinsa ga gidan Isra’ila;dukan iyakar duniya sun gaceton Allahnmu.4Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya,ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi;5ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya,da garaya da ƙarar rerawa,6tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago,ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki.7Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa,duniya da kuma kome da yake cikinta.8Bari koguna su tafa hannuwansu,bari duwatsu su rera tare don farin ciki;9bari su rera a gaban Ubangiji,gama yana zuwa domin yă hukunta duniya.Zai hukunta duniya da adalcimutane kuma cikin gaskiya.