Zabura88hau_bib

Waƙa ce, Zabura ta ’ya’yan Kora maza. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat leyannotmaskilna Heman dangin Ezra.

1Ya Ubangiji, Allah wanda ya cece ni,dare da rana ina kuka a gabanka.2Bari addu’ata ta zo a gabanka;ka kasa kunne ga kukata.
3Gama raina yana cike da wahalarayuwata tana gab da kabari.4An lissafta ni cikin waɗanda suka gangara zuwa cikin rami;ni kamar mutumin da ba shi da ƙarfi ne.5An ware ni tare da matattu,kamar waɗanda aka kashe da suke kwance a kabari,waɗanda ba ka ƙara tunawa,waɗanda aka yanke daga taimakonka.
6Ka sa ni a ramin da yake can ƙasacikin zurfafa mafi duhu.7Hasalarka tana da nauyi a kaina;ka turmushe ni da dukan raƙumanka. Sela8Ka ɗauke abokaina na kurkusa daga gare nika sa na zama abin ƙyama a gare su.An kange ni, ba yadda zan kuɓuta9idanuna ba sa gani sosai saboda baƙin ciki.Ina kira gare ka, ya Ubangiji, kowace rana;na tā da hannuwana zuwa gare ka.10Kakan nuna wa matattu ayyukanka na banmamaki ne?Waɗanda suka mutu sukan tashi su yabe ka ne? Sela11Ana furta ƙaunar a cikin kabari ne,ana zancen amincinka a cikin Hallaka ne?12An san ayyukanka masu banmamaki a wurin duhu ne,ko ayyukan adalcinka a lahira?
13Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji;da safe addu’ata kan zo gabanka.14Don me, ya Ubangiji, ka ƙi nika kuma ɓoye fuskarka daga gare ni?
15Tun ina ƙarami na sha wahala na kuma yi kusa in mutu;na sha wahalar razanarka kuma na kuma fid da zuciya.16Hasalarka ta sha kaina;razanarka ta hallaka ni.17Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa;sun mamaye ni ɗungum.18Ka ɗauke abokaina da ƙaunatattuna daga gare ni;duhu ne abokina na kurkusa.