Zabura87hau_bib
Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Waƙa ce.
1Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki.2Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyonafiye da dukan wuraren zaman Yaƙub.3Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da keYa birnin Allah, Sela4“Zan lissafta Rahaba cikin waɗanda suka san ni,Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush,zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’ ”5Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce,“Wannan da wancan an haifa a cikinta,Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.”6Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa,“An haifi wannan a Sihiyona.” Sela7Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera,“Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.”