Zabura84hau_bib
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit.Na ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce.
1Ina misalin kyan wurin zamanka,Ya Ubangiji Maɗaukaki!2Raina yana marmari, har yana suma,don filayen gidan Ubangiji;zuciyata da namana na tā da muryadomin Allah mai rai.3Har tsada ma ta sami gida,tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa,inda za tă ƙyanƙyashe ’ya’yanta,wuri kusa da bagadenka,Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna.4Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka;kullum suna ta yabonka. Sela5Masu albarka ne waɗanda ƙarfinsu yana daga gare ka,waɗanda suka kafa zukatansu a yin tafiya zuwa wuri mai tsarki ne.6Yayinda suke wuce ta Kwarin Baka,sukan mai da shi wurin maɓulɓulai;ruwan sama na farko kuma kan rufe shi da tafkuna.7Suna ta ƙara ƙarfi,har sai kowanne ya bayyana a gaban Allah a Sihiyona.8Ka ji addu’ata, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki;ka saurare ni, ya Allah na Yaƙub. Sela9Ka dubi garkuwarmu, ya Allah;ka duba da alheri a kan shafaffenka.10Rana guda a filayen gidan sun fidubu a wani wuri dabam;zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahnada in zauna a tentunan mugaye.11Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa;Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja;ba ya hana kowane abu mai kyauwa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.12Ya Ubangiji Maɗaukaki,mai albarka ne mutumin da ya dogara gare ka.