Zabura82hau_bib
Zabura ta Asaf.
1Allah yana shugabanta cikin babban taro;yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”.2“Har yaushe za ku kāre marasa adalciku kuma goyi bayan mugaye? Sela3Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu;ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.4Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata;ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.5“Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba.Suna yawo cikin duhu;an girgiza dukan tussan duniya.6“Na ce, ‘Ku “alloli” ne;dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne.7Amma za ku mutu kamar mutum kurum;za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.”8Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya,gama dukan al’ummai gādonka ne.