Zabura81hau_bib

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit.Ta Asaf.

1Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu;ku yi sowa ga Allah na Yaƙub!2Ku fara kaɗe-kaɗe, ku buga ganga,ku kaɗa garaya da molo masu daɗi.
3Ku busa ƙahon rago a Sabon Wata,da kuma sa’ad da wata ya kai tsakiya, a ranar Bikinmu;4wannan ƙa’ida ce domin Isra’ila,farilla ta Allah na Yaƙub.5Ya kafa shi a matsayin ƙa’ida domin Yusufsa’ad da ya fito daga Masar.Muka ji yaren da ba mu fahimta ba.
6Ya ce, “Na kau da nauyi daga kafaɗunku;an ’yantar da hannuwansu daga kwando.7Cikin damuwarku kun yi kira na kuwa kuɓutar da ku,na amsa muku daga girgijen tsawa;na gwada ku a ruwan Meriba. Sela
8“Ku ji, ya mutanena, zan kuwa gargaɗe ku,in ba za ku saurare ni ba, ya Isra’ila!9Kada ku kasance da baƙon allah a cikinku;ba za ku rusuna ga baƙon allah ba.10Ni ne Ubangiji Allahnkuwanda ya fitar da ku daga Masar.Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi.
11“Amma mutanena ba su saurare ni ba;Isra’ila bai miƙa kansa gare ni ba.12Saboda haka na ba da su ga zukatansu da suka tauraredon su bi dabararsu.
13“A ce mutanena za su saurare ni,a ce Isra’ila zai bi hanyoyina,14da nan da nan sai in rinjayi abokan gābansuin kuma juye hannuna a kan maƙiyansu!15Waɗanda suke ƙin Ubangiji za su fāɗi a gabansa da rawar jiki,hukuncinsu kuma zai dawwama har abada.16Amma za a ciyar da ku da alkama mafi kyau;da zuma daga dutsen da zai ƙosar da ku.”