Zabura67hau_bib
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura. Waƙa.
1Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace muyă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, Sela2don a san hanyoyinka a duniya,cetonka kuma a cikin dukan al’ummai.3Bari mutane su yabe ka, ya Allah;bari dukan mutane su yabe ka.4Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki,gama kana mulkin mutanenka da adalcikana kuma bi da al’umman duniya. Sela5Bari mutane su yabe ka, ya Allah;bari dukan mutane su yabe.6Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbintaAllah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu.7Allah yă sa mana albarka,dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.