Zabura64hau_bib
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
1Ka ji ni, ya Allah, yayinda nake faɗin abin da yake damuna;ka tsare raina daga barazanan abokin gāba.2Ka ɓoye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye,daga daure dauren wannan taro masu aikata mugunta.3Sukan wāsa harsunansu kamar takubasu harba kalmominsu kamar kibiyoyi masu kisa.4Sukan yin kwanto su harbi marar laifi;sukan yi harbi nan da nan, ba tsoro.5Sukan ƙarfafa juna a mugayen ƙulle-ƙullensu,sukan yi magana yadda za su ɓoye tarkunansu;su ce, “Wa zai gan su?”6Sukan yi ƙulle-ƙullen rashin adalci su ce,“Mun gama ƙulla cikakkiyar maƙarƙashiya tsab!”Zuciyar mutum da tunaninsa, suna da wuyar ganewa.7Amma Allah zai harbe su da kibiyoyi;nan da nan za a buge su su fāɗi.8Zai juya harshensu a kansuyă kuma kawo su ga hallaka;duk waɗanda suka gan su za su kaɗa kai, suna musu ba’a.9Dukan mutane za su ji tsoro;za su yi shelar ayyukan Allahsu kuma yi tunanin abin da ya aikata.10Bari masu adalci su yi farin ciki a cikin Ubangijisu kuma nemi mafaka a gare shi;bari dukan masu gaskiya a zuciya su yabe shi!