Zabura63hau_bib
Zabura ta Dawuda. Sa’ad da yake a hamadar Yahuda.
1Ya Allah, kai ne Allahna,da nacewa na neme ka;raina yana ƙishinka,jikina yana marmarinka,cikin busasshiyar ƙasar da ta zozayeinda babu ruwa.2Na gan ka a wuri mai tsarkina kuma dubi ikonka da ɗaukakarka.3Domin ƙaunarka ta fi rai kyau,leɓunana za su ɗaukaka ka.4Zan yabe ka muddin raina,kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.5Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau;da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.6A gadona na tuna da kai;ina tunaninka dukan dare.7Domin kai ne mai taimakona,ina rera a cikin inuwar fikafikanka.8Raina ya manne maka;hannunka na dama yana riƙe da ni.9Su da suke neman raina za su hallaka;za su gangara zuwa zurfafan duniya.10Za a bayar da su ga takobisu kuma zama abincin karnukan jeji.11Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah;dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi,amma za a rufe bakunan maƙaryata.