Zabura61hau_bib

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda.

1Ka ji kukata, ya Allah;ka saurari addu’ata.
2Daga iyakar duniya na yi kira gare ka,na yi kira yayinda zuciyata ta karai;ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi.3Gama kai ne mafakata,hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi.
4Ina marmari in zauna a tentinka har abadain sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. Sela5Gama ka ji alkawarina, ya Allah;ka ba ni gādo na waɗanda suke tsoron sunanka.
6Ka ƙara kwanakin ran sarki,shekarunsa su kasance a zamanai masu yawa.7Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada;ka sa ƙaunarka da amincinka su tsare shi.
8Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunankain kuma cika alkawarina kowace rana.