Zabura59hau_bib
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam.Sa’ad da Shawulu ya aiki mutane su yi tsaron gidan Dawuda don yă kashe shi.
1Ka cece ni daga abokan gābana, ya Allah;ka tsare ni daga waɗanda suka tayar mini.2Ka kuɓutar da ni daga masu aikata muguntaka kuma cece ni daga masu kisa.3Duba yadda suka kwanta suna jirana!Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da niba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji.4Ban yi wani laifi ba, duk da haka suna a shirye su fāɗa mini.Tashi ka taimake ni; dubi halin da nake ciki!5Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki,Allah na Isra’ila,ka tashi ka hukunta dukan al’ummai;kada ka nuna jinƙai ga mugaye maciya amana. Sela6Sukan dawo da yamma,suna wage haƙora kamar karnuka,suna yawo a birni.7Dubi abin da suke tofawa daga bakunansu,suna tofar da takuba daga leɓunansu,suna cewa, “Wa zai ji mu?”8Amma kai, ya Ubangiji, kakan yi musu dariya;kana yi wa dukan waɗannan al’ummai ba’a.9Ya ƙarfina, na dogara gare ka;kai, ya Allah, kai ne kagarata,10Allah mai ƙaunata.Allah zai sha gabanazai kuma sa in yi dariya a kan waɗanda suke magana marar kyau a kaina.11Amma kada ka kashe su, ya Ubangiji garkuwarmu,in ba haka mutanena za su manta.Cikin ikonka ka sa su yi ta yawo barkatai,ka kuma kawar da su.12Saboda zunuban bakunansu,saboda maganganun leɓunansu,bari a kama su cikin fariyarsu.Saboda zage-zage da ƙarairayin da suke yi,13ka cinye su da hasala,ka cinye su sarai.Sa’an nan za a sani a iyakar duniyacewa Allah yana mulki a bisa Yaƙub. Sela14Sukan dawo da yamma,suna wage haƙora kamar karnuka,suna yawo a birni.15Suna ta yawo neman abincisu kuwa yi haushi in ba su ƙoshi ba.16Amma zan rera game da ƙarfinka,da safe zan rera game da ƙaunarka;gama kai ne mafakata,kagarata a lokacin wahala.17Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka;kai, ya Allah, kai ne kagarata,Allah mai ƙaunata.