Zabura55hau_bib

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskilta Dawuda.

1Ka ji addu’ata, ya Allah,kada ka ƙyale roƙona;2ka ji ni ka kuma amsa mini.Tunanina yana damuna na kuma gaji tilis3hankalina ya tashi saboda yawan surutan masu ƙina,saboda danniyar mugaye.Gama sukan jawo mini wahala,suna jin haushina suna ƙina.
4Zuciyata tana wahala a cikina;tsorace-tsoracen mutuwa sun sha kaina.5Tsoro da rawan jiki sun kama ni;razana ta sha kaina.6Na ce, “Kash, da a ce ina da fikafikan kurciya mana!Ai, da na yi firiya na tafi na huta,7da na tafi can da nisana zauna a hamada; Sela8da na hanzarta na tafi wurin mafakata,nesa da muguwar iska da hadiri.”
9Ka rikitar da mugaye, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu,gama na ga rikici da faɗa a cikin birni.10Dare da rana suna yawo a kan katanga;mugun hali da zargi suna a cikinta.11Rundunar hallaka suna aiki a cikin birni;barazana da ƙarairayi ba sa taɓa barin titunanta.
12Da a ce abokin gāba ne ke zagina,da na jure da shi;da a ce maƙiyi yana tā da kansa a kaina,da na ɓoye daga gare shi.13Amma kai ne, mutum kamar ni,abokina, abokina na kurkusa,14wanda na taɓa jin daɗin zumunci da shi sosaiyayinda muke tafiya tarea taron jama’a a gidan Allah.
15Bari mutuwa ta ɗauki abokan gābana ba labari;bari su gangara da rai zuwa cikin kabari,gama mugunta tana samun masauƙi a cikinsu.
16Amma na kira ga Allah,Ubangiji kuwa ya cece ni.17Safe, rana da yammaina kuka da nishi,yakan kuwa ji muryata.18Yakan fisshe ni lafiyadaga yaƙin da ake yi da ni,ko da yake da yawa suna gāba da ni.19Allah, yana mulki har abada,zai ji su yă kuma azabtar da su, Selamutanen da ba sa taɓa canja hanyoyinsukuma ba sa tsoron Allah.
20Abokina ya kai wa abokansa hari;ya tā da alkawarinsa.21Maganarsa tana da laushi kamar man zaitun,duk da haka yaƙi yana a cikin zuciyarsa;kalmominsa sun fi mai sulɓi,duk da haka takuba ne zārarru.
22Ku kawo damuwoyinku ga Ubangijizai kuwa riƙe ku;ba zai taɓa barinmai adalci yă fāɗi ba.23Amma kai, ya Allah, za ka kawar da mugayezuwa cikin ramin lalacewa;masu kisa da mutane masu ruɗuba za su kai rabin kwanakin rayuwarsu ba.Amma ni dai, na dogara gare ka.