Zabura54hau_bib
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskilta Dawuda. Sa’ad da Zifawa suka tafi wurin Shawulu suka ce, “Ba Dawuda ba ne yake ɓuya a cikinmu?”
1Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka;ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka.2Ka ji addu’ata, ya Allah;ka saurari maganar bakina.3Baƙi suna kawo mini hari;mutane marasa imani suna neman raina,mutanen da ba sa tsoron Allah. Sela4Tabbatacce Allah ne mai taimakona,Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni.5Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina;cikin amincinka ka hallaka su.6Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka;zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau.7Gama ya cece ni daga dukan wahalolina,idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana.