Zabura52hau_bib

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Wani maskilta Dawuda. Sa’ad da Doyeg mutumin Edom ya tafi wurin Shawulu ya ce masa, “Dawuda ya tafi gidan Ahimelek.”

1Me ya sa kake fariya game da mugunta, kai babban mutum?Me ya sa kake fariya dukan yini,kai da kake abin kunya a idanun Allah?2Harshenka kan shirya hallaka;yana nan kamar reza mai ci,kana ta ruɗu.3Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri,ƙarya a maimakon faɗin gaskiya. Sela4Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa,Ya kai harshe mai ruɗu!
5Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka.Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka;zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. Sela6Masu adalci za su ga su ji tsoro;za su yi masa dariya, suna cewa,7“Yanzu, ga mutuminda bai mai da Allah mafakarsa baamma ya dogara a yawan arzikinsaya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!”
8Amma ni kamar itace zaitun neina haɓaka a gidan Allah;na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allahhar abada abadin.9Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi;a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau.Zan yabe ka a gaban tsarkakanka.