Zabura48hau_bib

Waƙa ce. Zabura ta ’ya’yan Kora maza.

1Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo,a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki.
2Kyakkyawa ce cikin tsayinta,abin farin cikin dukan duniya.Kamar ƙwanƙoli mafi tsayi na Zafon ne Dutsen Sihiyona,birnin Babban Sarki.3Allah yana cikin fadodinta;ya nuna kansa mafaka ce gare ta.
4Sa’ad da sarakuna suka haɗa rundunoni,sa’ad da suka yi gaba tare,5sun gan ta suka kuwa yi mamaki;suka gudu don tsoro.6Rawar jiki ya kama su a can,zafi kamar na mace mai naƙuda.7Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshishda iskar gabas ta wargaje.
8Yadda muka ji,haka muka gania cikin birnin Ubangiji Maɗaukaki,a cikin birnin Allahnmu.Allah ya sa ta zauna lafiyahar abada. Sela
9Cikin haikalinka, ya Allah,mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa.10Kamar sunanka, ya Allah,yabonka ya kai iyakokin duniya;hannunka na dama ya cika da adalci.11Dutsen Sihiyona ya yi farin ciki,ƙauyukan Yahuda suna murnasaboda hukuntanka.
12Yi tafiya cikin Sihiyona, ku kewaye ta,ku ƙirga hasumiyoyinta,13ku lura da katangarta da kyau,ku dubi fadodinta,don ku faɗe suga tsara mai zuwa.
14Gama wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin;zai zama jagorarmu har zuwa ƙarshe.