Zabura47hau_bib
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce.
1Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai;ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki.2Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne,Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya!3Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu,mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu.4Ya zaɓar mana gādonmu,abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. Sela5Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki,Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni.6Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai;ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai.7Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya;ku rera zabura ta yabo gare shi.8Allah yana mulki a bisa al’ummai;Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki.9Manyan mutanen al’ummai sun tarua matsayin mutanen Allah na Ibrahim,gama sarkunan duniya na Allah ne;ana ɗaukaka shi ƙwarai.