Zabura35hau_bib

Ta Dawuda.

1Yi hamayya, ya Ubangiji, da waɗanda suke hamayya da ni;yi faɗa da waɗanda suke faɗa da ni.2Ka ɗauki garkuwa da kuma makami;ka tashi ka taimake ni.3Ka ɗaga māshi da kuma abin da ake jefaa kan waɗanda suke fafarata.Ka ce wa raina,“Ni ne cetonka.”
4Bari waɗanda suke neman rainasu sha kunya a kuma kunyatar da su;bari waɗanda suke shirya lalacewatasu juya da baya su ruɗe.5Bari su zama kamar yayi a gaban iska,mala’ikan Ubangiji kuma yana korarsu;6bari hanyarsu tă yi duhu ta kuma yi santsi,mala’ikan Ubangiji kuma yana fafararsu.
7Da yake sun ɓoye tarko domina ba dalilikuma babu dalili suka haƙa mini rami,8bari lalaci yă kama su ba zato,bari tarkon da suka ɓoye yă kama su,bari su fāɗa cikin ramin, yă kai ga lalacinsu.9Sa’an nan raina zai cika da farin ciki a cikin Ubangijiin yi kuma murna a cikin cetonsa.10Dukan raina zai ce,“Wane ne kamar ka, ya Ubangiji?Ka kuɓutar da matalauta daga waɗanda suka fi ƙarfinsu,matalauta da masu bukata daga waɗanda suke musu fashi.”
11Shaidu marasa imani sun fito;suna mini tambaya a kan abubuwan da ban san kome a kai ba.12Suna sāka alherin da na yi musu da muguntasuka bar raina da nadama.13Duk da haka sa’ad da suke ciwo, na sanya rigar makokina ƙasƙantar da kaina da azumi.Sa’ad da aka mayar mini da addu’o’i babu amsa,14nakan yi ta yawo ina makokisai ka ce yadda nake yi wa abokina ko ɗan’uwana.Nakan sunkuyar da kaina cikin baƙin cikisai ka ce ina kuka domin mahaifiyata.15Amma sa’ad da na yi tuntuɓe, sukan taru suna murna;masu kai hari sun taru a kaina sa’ad da ban sani ba.Suna ɓata mini suna ba tsagaitawa.16Kamar marasa sani Allah suna mini riyar ba’a;Suna hararata da ƙiyayya.
17Ya Ubangiji, har yaushe za ka ci gaba da zuba ido kawai?Ka kuɓutar da raina daga farmakinsu,raina mai daraja daga waɗannan zakoki.18Zan yi godiya cikin taro mai girma;cikin ɗumbun mutane zan yabe ka.19Kada ka bar maƙaryatan nan,su yi farin ciki a kaina;kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili,su ji daɗin baƙin cikina.20Ba sa maganar salamasukan ƙirƙiro zage-zagen ƙaryaa kan waɗanda suka zama shiru a ƙasar.21Sukan wage mini bakinsu suna cewa, “Allah yă ƙara!Da idanunmu mun gani.”
22Ya Ubangiji, ka ga wannan; kada ka yi shiru.Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji.23Ka farka, ka kuma tashi ka kāre ni!Ka yi mini faɗa, ya Allahna da shugabana.24Ka nuna ni marar laifi ne ciki adalcinka,Ya Ubangiji Allahna; kada ka bari su yi farin ciki a kaina.25Kada ka bari su ce wa kansu, “Allah yă ƙara, dā ma abin da mun so ke nan!”Ko su ce, “Mun haɗiye shi.”
26Bari dukan waɗanda suke farin ciki a kaina a wahalatasu sha kunya su kuma ruɗe;bari dukan waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi nisu sha kunya da wulaƙanci.27Bari waɗanda suke murna saboda nasaratasu yi sowa don farin ciki da murna;bari kullum su riƙa cewa, “A ɗaukaka Ubangiji,wanda yake farin ciki da zaman lafiyar bawansa.”
28Harshena zai yi zancen adalcinkada kuma yabonka dukan yini.