Zabura32hau_bib

Ta Dawuda. Maskilne.

1Mai farin ciki ne shiwanda aka gafarta masa laifofinsa,wanda aka shafe zunubansa.2Mai farin ciki ne mutuminda Ubangiji ba ya lissafin zunubinsa a kansawanda kuma babu ruɗu a ruhunsa.
3Sa’ad da na yi shiru,ƙasusuwana sun yi ta mutuwacikin nishina dukan yini.4Gama dare da ranahannunka yana da nauyi a kaina;an shanye ƙarfina ƙafsai ka ce a zafin bazara. Sela
5Sa’an nan na furta zunubina a gare kaban kuwa ɓoye laifina ba.Na ce, “Zan furtalaifofina ga Ubangiji.”Ka kuwa gafartalaifin zunubina. Sela
6Saboda haka bari duk mai tsoron Allah yă yi addu’a gare kayayinda kake samuwa;tabbatacce sa’ad da manyan ruwaye suka taso,ba za su kai wurinsa ba.7Kai ne wurin ɓuyata;za ka tsare ni daga wahalaka kewaye ni da waƙoƙin ceto. Sela
8Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi;Zan ba ka shawara in kuma lura da kai.9Kada ka zama kamar doki ko doki,wanda ba su da azanciwanda dole sai an bi da su da linzami da ragamain ba haka ba, ba za su zo wurinka ba.10Azaban mugu da yawa suke,amma ƙaunar Ubangiji marar ƙarewakan kewaye mutumin da ya dogara gare shi.
11Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji ku kuma yi murna, ku adalai;ku rera, dukanku waɗanda zuciyarku take daidai!