Zabura27hau_bib
Ta Dawuda.
1Ubangiji ne haskena da cetona,wa zan ji tsoro?Ubangiji ne mafakar raina,wane ne zan ji tsoro?2Sa’ad da mugaye suka tasar minidon su cinye ni,sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari,sun yi tuntuɓe suka fāɗi.3Ko da yake mayaƙa sun kewaye ni,zuciyata ba za tă ji tsoro ba;ko da yake ya ɓarke a kaina,duk da haka zan ƙarfafa.4Abu guda na roƙi Ubangiji,wannan shi ne na nema,cewa in zauna a gidan Ubangijidukan kwanakin raina,in dubi kyan Ubangijiin kuma neme shi a cikin haikalinsa.5Gama a lokacin wahala,zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa;zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasaya kuma sa ni can a bisa dutse.6Sa’an nan kaina zai ɗaukakaa bisa abokan gābana waɗanda suka kewaye ni;a tabanakul nasa zan miƙa hadaya da sowa ta farin ciki;zan rera in kuma yi kiɗi ga Ubangiji.7Ka ji muryata sa’ad da na yi kira, ya Ubangiji;ka yi mini jinƙai ka kuma amsa mini.8Zuciyata kan faɗa game da kai, “Nemi fuskarsa!”Fuskarka, Ubangiji, zan nema.9Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni,kada ka kore bawanka daga gare ka cikin fushi;kai ne ka kasance mai taimakona.Kada ka ƙi ni ko ka yashe ni,Ya Allah Mai cetona.10Ko da mahaifina da mahaifiyata sun yashe ni,Ubangiji zai karɓe ni.11Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji;ka bi da ni a miƙaƙƙiyar hanyasaboda masu danne ni.12Kada ka ba da ni da sha’awar maƙiyina,gama masu shaidar ƙarya sun taso a kaina,suna numfasa tashin hankali.13Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewazan ga alherin Ubangiji;a ƙasar masu rai.14Ka dogara ga Ubangiji,ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciyaka kuma dogara ga Ubangiji.