Zabura2hau_bib
1Me ya sa ƙasashe suke haɗa bakimutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza?2Sarakunan duniya sun ɗauki matsayimasu mulki sun taru gaba ɗayasuna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.3Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu,mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.”4Mai zama a kursiyi a sama yana dariya;Ubangiji yana musu ba’a.5Sa’an nan ya tsawata musu cikin fushinsaya kuma razanar da su cikin hasalarsa, yana cewa,6“Na kafa Sarkina a kan kursiyia kan Sihiyona, dutsena mai tsarki.”7Sarki ya yi shelar umarnin Ubangiji.Ubangiji ya ce mini, “Kai Ɗana ne;yau na zama Mahaifinka.8Ka tambaye nizan kuwa sa al’ummai su zama gādonka,iyakokin duniya su zama mallakarka.9Za ka yi mulkinsu da sandan ƙarfe;za ka farfashe su kucu-kucu kamar tukunyar laka.”10Saboda haka, ku sarakuna, ku yi wayo;ku shiga hankalinku, ku masu mulkin duniya.11Ku bauta wa Ubangiji da tsoroku kuma yi farin ciki kuna rawar jiki.12Ku sumbaci Ɗan, don kada yă yi fushiku hallaka a abubuwan da kuke yi,gama fushinsa zai iya kuna farat ɗaya.Masu farin ciki ne dukan waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.