Zabura147hau_bib
1Yabi Ubangiji.Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu,abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi!2Ubangiji ya gina Urushalima;ya tattara kamammu na Isra’ilan da aka kai bauta.3Ya warkar da masu raunanar zuciyaya ɗaɗɗaura miyakunsu.4Ya lissafta yawan taurariya kuma kira kowannensu da suna.5Shugabanmu mai girma ne mai iko duka;ganewarsa ba shi da iyaka.6Ubangiji yana kula da masu sauƙinkaiyakan yar da mugaye a ƙasa.7Rera wa Ubangiji waƙar godiya;ku kada garaya ga Allahnmu.8Ya rufe sararin sama da gizagizai;yana tanada wa duniya ruwan samayana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai.9Yakan tanada wa shanu abincida kuma saboda ’ya’yan hankaki sa’ad da suka yi kira.10Jin daɗinsa ba ya a ƙarfin doki,balle farin cikinsa yă kasance a ƙafafun mutum;11Ubangiji yakan yi farin ciki a waɗanda suke tsoronsa,waɗanda suke sa zuciya a ƙaunarsa marar ƙarewa.12Ki ɗaukaka Ubangiji, ya Urushalima;ki yabi Allahnki, ya Sihiyona.13Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinkiyana kuma albarkace mutanenki a cikinki.14Yana ba da salama ga iyakokinkiyana kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.15Yana ba da umarninsa ga duniya;maganarsa tana tafiya da sauri.16Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar uluyă kuma watsar da hazo kamar toka.17Yana zuba ƙanƙara kamar ƙananan duwatsu.Wa zai iya jure wa sanyin da ya aiko?18Yakan aiki maganarsa ta kuwa narkar da su;yakan tā da iskarsa, ruwaye kuwa su gudu.19Ya bayyana maganarsa ga Yaƙub,dokokinsa da ƙa’idodinsa ga Isra’ila.20Bai yi wannan ga wata al’umma ba;ba su san dokokinsa ba.Yabi Ubangiji.