Zabura140hau_bib

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.

1Ka cece ni, ya Ubangiji, daga mugaye;ka tsare ni daga mutane masu rikici,2masu shirya maƙarƙashiya a zukatansusuna kuma kawo yaƙi kullum.3Suna sa harsunansu su yi kaifi kamar na maciji;dafin gamsheƙa yana a leɓunansu. Sela
4Ka kiyaye ni, ya Ubangiji, daga hannuwan mugaye;ka tsare ni daga mutane masu rikiciwaɗanda suke shirin kwashe ni a ƙafafu.5Masu girman kai sun sa mini tarko;sun shimfiɗa igiyoyin ragarsusun kuma shirya mini tarko a hanyata. Sela
6Ya Ubangiji, na ce maka, “Kai ne Allahna.”Ka ji kukata ta neman jinƙai, ya Ubangiji.7Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mai fansana mai ƙarfi,wanda yake garkuwoyin kaina a ranar yaƙi.8Kada ka biya wa mugaye bukatunsu, ya Ubangiji;kada ka bar shirinsu su yi nasara,in ba haka ba za su yi fariya. Sela
9Bari kawunan waɗanda suka kewaye nisu rufu da masifun da leɓunansu suka jawo.10Bari garwashin wuta yă zubo a kansu;bari a jefar da su cikin wuta,cikin rami mai zurfi, kada su sāke tashi.11Kada masu ɓata suna su taɓa kahu a ƙasar;bari masifa ta farauci mutane masu rikici.
12Na san cewa Ubangiji ya shirya wa matalauta adalciyana kuma yi wa mabukata adalci.13Tabbatacce masu adalci za su yabi sunankamasu aikata gaskiya kuma za su zauna a gabanka.