Zabura137hau_bib

1A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kukasa’ad da muka tuna da Sihiyona.2A can a kan rassan itatuwamuka rataye garayunmu,3gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi,masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki;suka ce, “Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!”
4Yaya za mu rera waƙoƙin Ubangijia baƙuwar ƙasa?5In na manta da ke, ya Urushalima,bari hannuna na dama manta da iyawarsa.6Bari harshena yă manne wa rufin bakinain ban tuna da ke ba,in ban so Urushalimafarin cikin mafi girma ba.
7Ka tuna, ya Ubangiji, abin da mutanen Edom suka yia ranar da Urushalima ta fāɗi.Suka yi ihu suka ce, “A ragargaza ta,A ragargaza ta har tushenta!”8Ya Diyar Babilon, an ƙaddara ke zuwa hallaka,mai farin ciki ne wanda ya sāka mikisaboda abin da kika yi mana,9shi da ya ƙwace jarirankiya fyaɗa su a kan duwatsu.