Zabura133hau_bib

Waƙar haurawa. Ta Dawuda.

1Abu mai kyau ne, mai daɗi kumasa’ad da ’yan’uwa suna zaman lafiya!
2Yana kamar mai mai darajar da aka zuba a kai,yana gangarawa a gemu,yana gangarawa a gemun Haruna,har zuwa wuyan rigunansa.3Yana kamar raɓar Hermonda take zubowa a kan Dutsen Sihiyona.Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa,har ma rai na har abada.