Zabura128hau_bib

Waƙar haurawa.

1Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji,waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.2Za ka ci amfanin aikinka;albarku da wadata za su zama naka.3Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’yaa cikin gidanka;’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitunkewaye da teburinka.4Ta haka mai albarka yakewanda yake tsoron Ubangiji.
5Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyonadukan kwanakin ranka;bari ka ga wadatar Urushalima,6bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka.Salama tă kasance tare da Isra’ila.