Zabura126hau_bib

Waƙar haurawa.

1Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona,mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki.2Bakunanmu sun cika da dariya,harsunanmu da waƙoƙin farin ciki.Sai ana faɗi a cikin al’ummai,“Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.”3Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu,mun kuwa cika da farin ciki.
4Ka maido da wadatarmu, ya Ubangijikamar rafuffuka a Negeb.5Waɗanda suka yi shuka da hawayeza su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.6Shi da ya fita yana kuka,riƙe da iri don shuki,zai dawo da waƙoƙin farin ciki,ɗauke da dammuna.