Zabura125hau_bib

Waƙar haurawa.

1Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona,wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada.2Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima,haka Ubangiji ya kewaye mutanensayanzu da har abada kuma.
3Sandar mulkin mugaye ba zai ci gaba da kasancea kan ƙasar da take rabon adalai ba,domin kada masu adalci su yi amfanida hannuwansu su aikata mugunta.
4Ka yi alheri, ya Ubangiji, ga waɗanda suke nagartattu,ga waɗanda suke masu aikata gaskiya a zuciyarsu.5Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyiUbangiji zai kore su tare da masu aikata mugunta.Salama tă kasance tare da Isra’ila.