Zabura122hau_bib

Waƙar haurawa. Ta Dawuda.

1Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni,“Bari mu tafi gidan Ubangiji.”2Ƙafafunmu suna tsayea ƙofofinki, ya Urushalima.
3An gina Urushalima kamar birninda aka yi a harhaɗe wuri guda.4A can ne kabilu suke haurawa,kabilan Ubangiji,don su yabi sunan Ubangijibisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila.5A can kursiyoyin shari’a yake tsaye,kursiyoyin gidan Dawuda.
6Ku yi addu’a don salamar Urushalima,“Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya.7Bari salama ta kasance a katangarkizaman lafiya kuma a fadodinki.”8Saboda ’yan’uwana da kuma abokaina,zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.”9Saboda gidan Ubangiji Allahnmu,zan nemi wadatarki.