Zabura120hau_bib

Waƙar haurawa.

1Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata,ya kuwa amsa mini.2Ka cece ni, ya Ubangiji,daga leɓuna masu ƙaryada kuma daga harsuna masu yaudara.
3Me zai yi maka,me kuma ya fi,ya kai harshe mai yaudara?4Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi,tare da garwashin wuta na itacen tsintsiya.
5Kaitona da nake zama a Meshek,da nake zama a ciki tentunan Kedar!6Da daɗewa na zaunaa cikin waɗanda suke ƙin salama.7Ni mutum ne mai salama;amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi.