Zabura113hau_bib

1Yabi Ubangiji.Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji,ku yabi sunan Ubangiji.2Bari a yabi sunan Ubangiji,yanzu da har abada kuma.3Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa,a yabi sunan Ubangiji.
4Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai,ɗaukakarsa a bisa sammai5Wane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu,Wannan mai zama a kursiyi can bisa,6wanda yake sunkuya yă dubisammai da duniya?
7Yakan tā da matalauta daga ƙurayakan ɗaga mabukata daga tarin toka;8ya zaunar da su tare da sarakuna,tare da sarakunan mutanensu.9Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidantata zama kamar mahaifiyar ’ya’ya mai farin ciki.Yabi Ubangiji.