Zabura111hau_bib

1Yabi Ubangiji.Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyataa cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro.
2Ayyukan Ubangiji da girma suke;dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu.3Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne,adalcinsa kuma zai dawwama har abada.4Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa;Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma.5Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa;yakan tuna da alkawarinsa har abada.
6Ya nuna wa mutanensa ikon ayyukansa,yana ba su ƙasashen waɗansu al’ummai.7Ayyukan hannuwansa masu aminci ne da kuma gaskiya;dukan farillansa abin dogara ne.8Tsayayyu ne har abada abadin,ana yinsu cikin aminci da kuma gaskiya.9Yana ba da ceto ga mutanensa;ya kafa alkawarinsa har abada,tsarki da banrazana ne sunansa.
10Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima;dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau.Gare shi ne madawwamin yabo.