Zabura110hau_bib

Ta Dawuda. Zabura ce.

1Ubangiji ya ce wa Ubangijina,“Zauna a hannun damana,sai na sa abokan gābankasu zama matashin sawunka.”
2Ubangiji zai fadada ikon sandan mulkinka daga Sihiyonaza ka yi mulki a tsakiyar abokan gābanka.3Rundunarka za su so yin yaƙia ranarka ta yaƙi.Saye cikin ɗaukaka mai tsarki,daga cikin ciki na safiyaza ka karɓi raɓar ƙuruciyarka.
4Ubangiji ya rantseba zai kuma canja zuciyarsa ba,“Kai firist ne har abada,bisa ga tsarin Melkizedek.”
5Ubangiji yana a hannun damanka;zai murƙushe sarakuna a ranar fushinsa.6Zai hukunta al’ummai, yana tarawa gawawwakiyana kuma murƙushe masu mulkin dukan duniya.7Zai sha daga rafin da yake kusa da hanya;saboda haka zai ɗaga kansa sama.