Zabura11hau_bib
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don busa. Ta Dawuda.
1A wurin Ubangiji ne nake samun mafaka.Yaya za ku ce mini,“Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu.2Gama duba, mugaye sun tanƙware bakkunansu;sun kuma ɗana kibiyoyinsudon su harbi mutanen kirki a zuciyadaga cikin duhu.3Sa’ad da aka tumɓuke tushe,me adali zai iya yi?”4Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki;Ubangiji yana a kursiyinsa a sama.Yana kallon ’ya’yan mutane;idanunsa suna bincike su.5Ubangiji yana bincike adalai,amma ransa yana ƙi mugayeda masu son rikici.6A kan mugaye zai zubagarwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu;iska mai zafi zai zama rabonsu.7Gama Ubangiji mai adalci ne,yana ƙaunar gaskiyamasu adalci za su ga fuskarsa.