Zabura102hau_bib
Addu’ar mutum mai shan wahala. Sa’ad da ya rasa ƙarfi ya kuma yi makoki a gaban Ubangiji.
1Ka ji addu’ata, ya Ubangiji;bari kukata ta neman taimako ta zo gare ka.2Kada ka ɓoye fuskarka daga gare nisa’ad da nake cikin damuwa.Ka juye kunnenka gare ni;sa’ad da na yi kira, ka amsa mini da sauri.3Gama kwanakina sun ɓace kamar hayaƙi;ƙasusuwana suna ƙuna kamar jan wuta.4Zuciyata ta kamu da ciwo ta kuma bushe kamar ciyawa;na manta in ci abinci.5Saboda nishina mai ƙarfina rame na bar ƙasusuwa kawai.6Ni kamar mujiyar jeji ne,kamar mujiya a kufai.7Na kwanta a faɗake; na zamakamar tsuntsun da yake shi kaɗai a kan rufin ɗaki.8Dukan yini abokan gābana suna tsokanata;waɗanda suke mini ba’a suna amfani da sunana yă zama abin la’ana.9Gama ina cin toka a matsayin abincinaina kuma gauraye abin sha nawa da hawaye10saboda fushinka mai girma,gama ka ɗaga ni sama ka yar a gefe.11Kwanakina suna kamar inuwar yamma;na bushe kamar ciyawa.12Amma kai, ya Ubangiji, kana zaune a kursiyinka har abada;sunan da ka yi zai dawwama a dukan zamanai.13Za ka tashi ka kuma ji tausayin Sihiyona,gama lokaci ne na nuna alheri gare ta;ƙayyadadden lokacin ya zo.14Gama duwatsunta suna da daraja ga bayinka;ƙurarta kawai kan sa su ji tausayi.15Al’ummai za su ji tsoron sunan Ubangiji,dukan sarakunan duniya za su girmama ɗaukakarka.16Gama Ubangiji zai sāke gina Sihiyonaya kuma bayyana a ɗaukakarsa.17Zai amsa addu’ar marasa ƙarfi;ba zai ƙyale roƙonsu ba.18Bari a rubuta wannan don tsara mai zuwa,cewa mutanen da ba a riga an halitta ba za su yabi Ubangiji,19“Ubangiji ya duba ƙasa daga wurinsa mai tsarki a bisa,daga sama ya hangi duniya,20don yă ji nishe-nishen ’yan kurkukuyă kuma saki waɗanda aka yanke musu hukuncin mutuwa.”21Saboda haka za a furta sunan Ubangiji a Sihiyonayabonsa kuma a Urushalima22sa’ad da mutane da mulkokisuka tattaru don su yi wa Ubangiji sujada.23Cikin rayuwata, ya karye ƙarfina;ya gajartar da kwanakina.24Sai na ce,“Kada ka ɗauke ni a tsakiyar kwanakina, ya Allah;shekarunka suna bi cikin dukan zamanai.25A farkon fari ka kafa tushen duniya,sammai kuma aikin hannuwanka ne.26Za su hallaka, amma za ka ci gaba;duk za su tsufe kamar riga.Kamar riga za ka canja suza a kuwa zubar da su.27Amma kana nan yadda kake,kuma shekarunka ba za su taɓa ƙarewa ba.28’Ya’yan bayinka za su zauna a gabanka;zuriyarsu za su kahu a gabanka.”