Zabura101hau_bib

Ta Dawuda. Zabura ce.

1Zan rera wa ƙauna da adalcinka;gare ka, ya Ubangiji, zan rera yabo.2Zan yi hankali ga yin rayuwa marar zargi,yaushe za ka zo gare ni?Zan bi da sha’anin gidanada zuciya marar abin zargi3Ba zan kafa a gaban idanuna 1wani abu marar kyau ba.Na ƙi jinin ayyukan mutane marasa aminci;ba za su manne mini ba.4Mutane masu mugun zuciya za su nesa da ni;ba abin da zai haɗa ni da mugunta.
5Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoyeshi za a kashe;duk mai renin wayo da mai girman kai,ba zan jure masa ba.
6Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar,don su zauna tare da ni;tafiyarsa ba ta da zargizai yi mini hidima.
7Babu mai ruɗunda zai zauna a gidana;babu mai ƙaryanda zai tsaya a gabana.
8Kowace safiya zan rufe bakunandukan mugaye a ƙasar;zan yanke kowane mai aikata muguntadaga birnin Ubangiji.