Zabura100hau_bib

Zabura ce. Don yin godiya.

1Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya.2Yi wa Ubangiji sujada da murna;ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.3Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah.Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne;mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa.
4Ku shiga ƙofofinsa da godiyafilayen gidansa kuma da yabo;ku gode masa ku kuma yabi sunansa.5Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada;amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.