Karin Magana31hau_bib

1Maganganun Sarki Lemuwel, magana ce horarriyamahaifiyarsa ta koya masa,2“Ka saurara, ya ɗana! Ka saurara, ɗan cikina!Ka saurara, ya ɗan amshin addu’ata!3Kada ka ba da ƙarfinka a kan mata,ƙarfinka ga waɗanda suka hallaka sarakuna.
4“Ba na sarakuna ba ne, ya Lemuwel,ba na sarakuna ba ne su sha ruwan inabi,ba na masu mulki ba ne su yi marmarin barasa,5don kada su sha su manta da abin da doka ta umarta,su hana wa waɗanda aka danne hakkinsu.6A ba da barasa ga waɗanda suke cikin halin ƙaƙa naka yi,ruwan inabi ga waɗanda suke cikin wahala;7bari su sha su manta da talaucinsukada kuma su ƙara tunawa da ɓacin ransu.
8“Yi magana domin bebaye,domin hakkin dukan waɗanda suke naƙasassu.9Yi magana a kuma yi shari’ar adalci;a tsare hakkin talakawa da masu bukata.”10Wa yake iya samun mace mai halin kirki?Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai.11Mijinta yana da cikakken amincewa da itakuma ba ya rasa wani abu mai daraja.12Takan yi masa alheri ba mugunta ba,dukan kwanakin ranta.13Takan zaɓi ulu da lilinta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki.14Ita kamar jirgin ’yan kasuwa netana kawo abincinta daga nesa.15Takan farka tun da sauran duhu;ta tanada wa iyalinta abincita kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.16Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta;daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.17Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru;hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.18Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta,kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.19Da hannunta take riƙe abin kaɗita kuma kama abin saƙa da yatsotsinta.20Takan marabci talakawatakan kuma taimaki masu bukata.21Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro saboda gidanta;gama dukansu suna da tufafi masu kauri.22Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa;tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.23Ana girmama mijinta a ƙofar shiga birniinda yakan zauna a cikin dattawan gari.24Takan yi riguna na lilin ta sayar;takan kuma sayar wa ’yan kasuwa da ɗamara.25Ƙarfi da mutunci su ne suturarta;za tă iya yin dariyar kwanaki masu zuwa.26Tana magana da hikima,kuma umarnai mai aminci yana a harshenta.27Tana lura da sha’anin gidantakuma ba ta cin abincin ƙyuya.28’Ya’yanta sukan tashi su ce da ita mai albarka;haka mijinta ma, yakan kuma yabe ta yana cewa,29“Mata da yawa suna yin abubuwan yabo,amma ke kin fi su duka.”30Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe;amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce.31Ka ba ta ladar da ya dace tă samo wa kanta,bari kuma ayyukanta su kawo mata yabo a ƙofar shiga birni.