Mika4hau_bib

Dutsen Ubangiji

1A kwanakin ƙarsheza a kafa dutsen haikalin Ubangijiyă zama babba a cikin duwatsu.Za a ɗaga shi sama da tuddai,mutane kuma za su riƙa ɗunguma zuwa gare shi.2Al’ummai da yawa za su zo su ce,“Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji,zuwa gidan Allah na Yaƙub.Zai koya mana hanyoyinsa,don mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.”Doka za tă fita daga Sihiyona,maganar Ubangiji kuma daga Urushalima.3Zai shari’anta tsakanin mutaneyă kuma sulhunta tsakanin manyan al’ummai nesa da kuma kusa.Har su mai da takubansu su zama garemani,māsunsu kuma su zama wuƙaƙen askin itace.Al’umma ba za tă ɗauki takobi gāba da wata al’umma ba,ko a yi horarwa don yaƙi.4Kowa zai zauna a tushen kuringar inabinsada tushen ɓaurensa,kuma ba wanda zai tsoratar da su,gama Ubangiji Maɗaukaki ne ya faɗa.5Dukan al’ummai za su iya tafiyaa cikin sunan allolinsu;mu dai za mu yi tafiya a cikin sunan UbangijiAllahnmu har abada abadin.

Shirin Ubangiji

6“A wannan rana,” in ji Ubangiji,“zan tattara guragu;zan kuma tara masu zaman bauta,da waɗanda na sa suka damu.7Zan mai da guragu su zama raguwa,waɗanda aka kora, su zama al’umma mai ƙarfi.Ubangiji zai yi mulkinsu a Dutsen Sihiyonadaga wannan rana da kuma har abada.8Game da ke, ya hasumiyar tsaron garke,Ya mafaka Diyar Sihiyona,za a maido miki da mulkinki na dā,sarauta kuma za tă zo wa Diyar Urushalima.”
9Don me yanzu kike kuka da ƙarfi,ba ki da sarki ne?Masu shawararki sun hallaka ne,da zafi ya cika ki kamar mace mai naƙuda?10Ki yi birgima cikin zafin azaba, ya Diyar Sihiyona,kamar macen da take naƙuda,don yanzu dole ki bar birniki kafa sansani a filin Allah.Za ki tafi Babilon;a can za a kuɓutar da ki.A can ne Ubangijizai fanshe ki daga hannun maƙiyanki.
11Amma yanzu al’ummai da yawasuna gāba da ke.Suna cewa, “Bari a ƙazantar da ita,bari mu zuba wa Sihiyona ido.”12Amma ba su santunanin Ubangiji ba;ba su fahimci shirinsa ba,shi da ya tattara su kamar dammuna a masussuka.13“Ki tashi ki yi sussuka, ya Diyar Sihiyona,gama zan ba ki ƙahonin ƙarfe;zan ba ki kofatan tagulladomin ki ragargaje al’ummai masu yawa.”Za ki ba Ubangiji dukan dukiyarsu da suka tara ta hanyar zamba,wadatarsu kuma ga Ubangiji dukan duniya.