Makoki4hau_bib
1Zinariya ta rasa kyanta,hasken zinariya ya dushe!An warwatsar da tsarkakakkun duwatsumasu daraja a kan tituna.2Dubi samarin Sihiyona masu daraja,waɗanda a dā darajarsu ta isa nauyin zinariya,yanzu ana ɗaukar su a matsayin tukwanen ƙasa,aikin maginin tukwane!3Ko diloli suna ba ’ya’yansu nono su sha,amma mutanena sun zama marasa zuciyakamar jiminai a cikin jeji.4Domin ƙishirwaharshen jarirai ya manne a rufin bakinsu;yaran suna roƙo a ba su burodi,amma ba wanda ya ba su.5Waɗanda a dā sukan ci abinci mai daɗiyanzu su ne masu bara a tituna.Waɗanda a dā suke sa kaya masu kyauyanzu suna kwance a kan tarin toka.6Horon mutanenaya fi na Sodom girma,wadda aka hallaka farat ɗayaba wani hannu da ya juya ya taimake ta.7’Ya’yan sarakunansu sun fi ƙanƙara haskesun kuma fi madara fari,jikunansu sun fi murjani ja,kyansu kamar shuɗin yakutu.8Amma yanzu sun fi dare duhu;ba a iya gane su a tituna.Fatar jikinsu ta manne da ƙasusuwansu;sun bushe kamar itace.9Gara waɗanda aka kashe su da takobida waɗanda suke mutuwa da yunwa;sun rame domin rashin abinci a gona.10Da hannuwansu mata masu tausayisun dafa yaransu,suka zama masu abincisa’ad da aka hallaka mutanena.11Ubangiji ya saki fushinsa;ya zuba zafin fushinsa.Ya hura wuta a Sihiyonata kuma cinye harsashin gininta.12Sarakunan duniya ba su gaskata ba,haka ma mutanen duniya,cewa magabta da maƙiyaza su iya shiga ƙofofin Urushalima.13Amma ya faru domin zunuban annabawantada muguntar firistocinta,waɗanda suka zubda jinin masu adalci a cikinsu.14Yanzu suna yawo barkatai a titunakamar makafi.Sun ƙazantu da jiniyadda ba wanda zai kuskura ya taɓa rigunansu.15“Ku tafi! Ba ku da tsabta!” Haka mutane suke ihu suke ce musu.“Ku tashi daga nan! Ku tashi daga nan! Kada ku taɓa mu!”Sa’ad da suka gudu suna yawo,mutanen waɗansu ƙasashe suka ce,“Ba za su ci gaba da zama a nan ba.”16Ubangiji kansa ya warwatsa su;ya daina duban su.Ba a ba firistoci girma,ba su ba dattawa gata.17Idanunmu sun gaji,suna ta dubawa ko taimako zai zo;mu sa ido ko za mu gaƙasar da za tă iya taimakon mu.18Ana bin sawunmu,ba za mu iya tafiya kan tituna ba.Ƙarshenmu ya kusa, kwanakinmu sun ƙare,gama ƙarshenmu ya zo.19Masu fafarar mu sun fi gaggafamai firiya a sararin sama sauri;sun fafare mu a kan duwatsusuna fakon mu a jeji.20Shafaffe na Ubangiji, numfashin ranmu,ya fāɗi cikin tarkonsu.Muna tunani cewa za mu iya rayuwacikin sauran mutane a ƙarƙashin inuwarsa.21Ku yi murna da farin ciki, ya Diyar Edom,ke mai zama a ƙasar Uz.Amma ke ma za a ba ki kwaf;za ki bugu ki zama tsirara.22Ya Diyar Sihiyona, hukuncinki zai ƙare;ba zai sa zaman bautarki yă yi tsayi ba.Amma ya Diyar Edom, zai hukunta zunubinkiyă tona tsiraicinki.