Makoki2hau_bib

1Yadda Ubangiji ya rufe Diyar Sihiyonada gizagizan fushi!Ya jefar da darajar Isra’iladaga sama zuwa ƙasa;bai tuna da wurin ɗora ƙafafunsa baa ranar fushinsa.
2Ubangiji ya hallakarda wurin zaman Yaƙub ba tausayi;A cikin fushinsa kuma zai rurrushekagaran Diyar Yahuda.Ya ƙasƙantar da mulkida masu mulki.
3A cikin zafin fushi ya fasakowane ƙaho na Isra’ila.Ya janye hannun damansasa’ad da maƙiyi ya zo.Ya yi ƙuna a cikin Yaƙub kamar wuta mai ƙoneduk abin da yake kusa da ita.
4Kamar abokin gāba, ya ɗana bakansa;hannun damansa na shirye.Kamar maƙiyi,ya kashe duk wanda idonsa ya ji daɗin gani;ya zuba fushinsa kamar wutaa kan tenti na Diyar Sihiyona.
5Ubangiji kamar maƙiyi ne;ya hallaka Isra’ila.Ya hallaka wurarenta dukaya kuma hallaka kagaranta.Ya ƙara yawan makoki da baƙin cikiwa Diyar Yahuda.
6Ya rushe haikalinsa kamar lambu;ya hallaka wurin yi masa sujada.Ubangiji ya sa Sihiyona ta mantada bukukkuwanta da kuma ranakunta na Asabbaci;a cikin zafin fushinsaya watsar da sarki da firist.
7Ubangiji ya ƙi bagadensaya kuma yi wofi da haikalinsa.Ya ba maƙiyinta fadodinta;suka yi sowa a cikin gidan Ubangijikamar a ranar da ake yin biki.
8Ubangiji ya ƙuduri niyya yă rushe bangonda yake kewaye da Diyar Sihiyona.Ya auna da igiyar awobai fasa hallaka ta ba.Ya sa katanga da katangaduk suka lalace.
9Ƙofofinta sun nutse a cikin ƙasa;ya kakkarya ƙarafanta.Sarakunanta da ’ya’yan sarakunantaduk an kai su bauta cikin waɗansu ƙasashe,babu sauran doka,annabawa kuma ba su samunwahayi daga wurin Ubangiji.
10Dattawan Diyar Sihiyonasun zauna shiru a ƙasa;suka kuma sa rigar buhu.’Yan matan Urushalima sukasunkuyar da kawunansu ƙasa.
11Idanuna sun dushe don yawan kuka,raina na cike da baƙin ciki;zuciyata ta karayadomin mutanena sun hallaka,domin yara da jarirai suna sumaa kan hanyoyi a cikin birni.
12Suna ce wa uwayensu,“Ina burodi da ruwan inabi?”Yayinda suke suma kamar mutanenda aka ji masu ciwo a cikin birni,sa’ad da suke mutuwaa hannuwan uwayensu.
13Me zan ce miki?Da me zan kwatanta ki,ke Diyar Urushalima?Da me zan misalta ki,yadda zan iya yi miki ta’aziyya,Ke Budurwa Diyar Sihiyona?Ciwonki yana da zurfi kamar teku.Wane ne zai iya warkar da ke?
14Wahayin annabawankiƙarya ne kuma marasa amfani;ba su tona zunubanki bayadda za su iya ceto ki daga bauta ba.Sun yi miki annabcin ƙaryamarar amfani.
15Duk masu wucewasuna yi miki tafi na reni;suna yi wa Diyar Urushalimatsaki suna kaɗa kai suna cewa,“Wannan ne birnin da aka cekyakkyawa ne,mai farantawa dukan duniya rai?”
16Maƙiyanki duka suna ta surutugame da ke;suna tsaki suna cizon haƙorasuna cewa, “Mun hallaka ta.Wannan ce ranar da muke jira;yau mun gan ta.”
17Ubangiji ya yi abin da ya shirya;ya cika maganarsa,wadda ya umarta tun daɗewa.Ya jefar da ke ba tausayi,ya bari maƙiya sun yi nasara da ke,ya ɗaukaka ƙahon maƙiyanki.
18Zuciyar mutaneta yi kuka ga Ubangiji.Ya bangon Diyar Urushalima,bar hawayenki su zuba kamar rafidare da rana;kada ki huta,kada idanunki su huta.
19Ki tashi, ki yi kuka cikin dare,dare na yi sai ki fara kuka;kina buɗewa Ubangiji zuciyarki.Ki ɗaga hannuwanki gare shidomin rayukan ’ya’yanki,waɗanda suka suma don yunwaa kan kowane titi.
20“Ka duba, ka gani ya Ubangiji.Wane ne ka taɓa yi wa haka?Ko ya kamata uwaye su ci ’ya’yansu,’ya’yan da suka yi reno?Ko ya kamata a kashe firistoci da annabawaa cikin haikalin Ubangiji?
21“Matasa da tsofaffi duksuna kwanciya a cikin ƙurar tituna;an karkashe matasada ’yan matana da takobi.Ka kashe su a ranar fushinka;ka kashe su ba tausayi.
22“Kamar yadda kake yin gayyata a ranar biki,haka kake kawo mini tsoro a kowane gefe.A ranar fushin Ubangijiba mai tserewa ba wanda zai tsira;maƙiyina ya kashe waɗanda na yi renonsu,na kuma lura da su.”