Makoki1hau_bib
1Yanzu birnin ya zama babu kowa a ciki,birnin da a dā yake cike da mutane!Yanzu birnin ya zama kamar gwauruwa,wadda a dā babba ce ita a cikin ƙasashe!Ita da take sarauniya a cikin lardunayanzu ta zama baiwa.2Tana yin kuka mai zafi da dare,hawaye na gangara a kan kumatunta.A cikin masoyanta dukababu wanda ya yi mata ta’aziyya.Duk abokanta sun yashe ta;sun zama abokan gābanta.3Bayan wahala da baƙin ciki,Yahuda ta tafi bauta.Ta zauna a cikin ƙasashe,ba tă samu wurin hutawa ba.Duk masu fafararta sun same tasa’ad da take cikin matuƙar ɓacin rai.4Hanyoyin zuwa Sihiyona suna makoki,gama ba wanda ya zo bikin da ta shirya.Ba kowa a hanyoyin shiganta.Firistocinta suna gurnani,’yan matana kuma suna wahala,kuma tana cikin shan wahala ƙwarai.5Maƙiyanta sun zama shugabanninta;Abokan gābanta suna da kwanciyar rai.Ubangiji ya kawo mata ɓacin raidomin yawan zunubanta.’Ya’yanta sun tafi bauta,a ƙarƙashin maƙiyanta.6Diyar Sihiyona ba tada sauran daraja.’Ya’yan sarakunanta sun zama kamar bareyiwaɗanda suka rasa wurin kiwo;cikin rashin ƙarfi suka gujewa masu fafararsu.7A cikin kwanakin da take shan wahala take kuma yawoUrushalima ta tuna da dukan dukiyarda take da ita a kwanakin dā can.Sa’ad da mutanenta suka faɗa cikin hannun abokan gābanta,ba wanda ya taimake ta.Maƙiyanta suka dube tasuka yi mata dariya don hallakar da ta auko mata.8Urushalima ta yi zunubi ƙwaraisaboda haka ta zama marar tsarki.Dukan masu martaba ta sun raina ta,gama sun ga tsiraicinta;ita ma da kanta tana nishi da ƙyarta kuma juya baya.9Ƙazantarta ta manne wa rigunanta;ba tă kula da nan gaba ba,fāɗuwarta kuwa babban abu ne;babu wanda zai yi mata ta’aziyya.“Duba, ya Ubangiji, ka ga wahalata,gama maƙiyi ya yi nasara.”10Maƙiya ya kwashedukiyarta duka;ta ga mutanen da ba su san Allah basun shiga wuri mai tsarkintawaɗanda ka hana sushiga taron jama’arka.11Dukan mutanenta suna nishida ƙyar suna neman burodi;sun sayar da dukiyarsu don su samu abincidon kada su mutu da yunwa.“Ubangiji, ka duba ka gani,gama an yashe ni.”12“Ko wannan ba wani abu ba ne a wurinku, dukanku masu wucewa?Ku duba ku gani.Ko akwai wata wahala kamaririn wadda nake sha,wadda Ubangiji ya auko minia cikin zafin fushinsa?13“Daga sama ya aiko da wuta,ya aiko ta cikin ƙasusuwana.Ya shimfiɗa raga a ƙafafunaya juyo da ni.Ya bar ni ni kaɗai,sumamme dukan yini.14“Ya ɗaura zunubaina a wuyana;aka naɗe su a hannuwansa.Aka rataye su a wuyanaUbangiji ya kwashe ƙarfina.Ya bashe niga waɗanda suka fi ni ƙarfi.15“Ubangiji ya ƙiduk mayaƙan da suke tare da ni;ya sa wata runduna ta tayar minita kuma tattake samarina.Ubangiji ya tattake budurwa Diyar Yahudakamar ’ya’yan inabi a wurin matsewa.16“Dalilin da ya sa nake kuka ke nanidanuna kuma suna ta zubar da hawaye.Babu wani a kusa da zai yi mini ta’aziyya,ba wanda zai sabunta ruhuna.’Ya’yana sun zama fakiraidomin maƙiyina ya yi nasara.”17Sihiyona ta miƙa hannunta,amma ba wani da zai yi mata ta’aziyya.Ubangiji ya umarta cewamaƙwabtansa za su zama maƙiyansa;Urushalima ta zamaabar ƙyama a cikinsu.18“Ubangiji mai adalci ne,duk da haka na yi tawaye da umarninsa.Ku saurara, jama’a duka;ku dubi wahalar da nake sha.Samarina da ’yan matanaduka sun tafi bauta.19“Na kira abokainaamma sun yashe ni.Firistocina da dattawanasun hallaka a cikin birninyayinda suke neman abincidon kada su mutu da yunwa.20“Duba, Ubangiji, ka ga ƙuncin da nake ciki!Ina shan azaba a raina,ba ni da kwanciyar rai a cikin zuciyata,domin na yi tawaye sosai.A waje takobi na kisa;a ciki kuma akwai mutuwa.21“Mutane suna ji ina nishi da ƙyar,amma ba wanda zai yi mini ta’aziyya.Dukan maƙiyana sun ji wahalar da nake ciki;suna farin ciki da abin da ka yi.Ka kawo ranan nan da ka sanardomin su ma su zama kamar ni.22“Bari ka ga muguntarsu duka;ka yi musuyadda ka yi minidomin dukan zunubansu.Nishina da yawakuma zuciyata ta gaji.”