Yowel2hau_bib

Rundunar fāra

1Ku busa ƙaho a cikin Sihiyona;ku yi karar amo a tsaunina mai tsarki.Bari dukan mazaunan ƙasar su yi rawan jiki,gama ranar Ubangiji tana zuwa.Tana gab da faruwa2rana ce ta baƙin duhu ƙirin,ranar gizagizai ce baƙi ƙirin.Babbar rundunar mayaƙa mai ƙarfi tana zuwakamar ketowar alfijir a kan duwatsuyadda ba a taɓa ganin irinta ba,ba kuwa za a ƙara ganin irinta ba har tsararraki masu zuwa.
3A gabansu wuta tana ci,a bayansu ga harshen wuta yana ci,A gabansu ƙasa ta yi kamar gonar Eden,a bayansu kuma jeji ne wofi,babu abin da ya kuɓuce musu.4Suna da kamannin dawakai;suna gudu kamar dokin yaƙi.5Da motsi kamar na kekunan yaƙisun tsallake ƙwanƙolin duwatsu,kamar ƙarar harshen wuta mai cin tattaka,kamar runduna mai ƙarfi wadda ta ja dāgār yaƙi.
6Da ganinsu, al’ummai sun kamu da azaba;kowace fuska ta yanƙwane.7Sukan auka kamar jarumawa;sukan hau katanga kamar sojoji.Kowa yana takawa bisa ga tsari,ba mai kaucewa.8Ba sa turin juna,kowane yakan miƙe gaba.Sukan kutsa cikin abokan gābaba mai tsai da su.9Sukan ruga cikin birni,suna gudu a kan katanga.Sukan hau gidaje,sukan shiga ta tagogi kamar ɓarayi.
10A gabansu duniya takan girgiza,sararin sama kuma yakan jijjigu,rana da wata su yi duhu,taurari kuma ba sa ba da haske.11Ubangiji ya yi tsawawa shugaban mayaƙansa;sojojinsa sun fi a ƙirgemasu ƙarfi ne kuma su waɗanda suke biyayya da umarninsa.Ranar Ubangiji da girma take;mai banrazana.Wa zai iya jure mata?

Ku kyakkece zuciyarku

12“Ko yanzu”, in ji Ubangiji,“Ku juyo gare ni da dukan zuciyarku,da azumi da kuka da makoki.”
13Ku kyakkece zuciyarkuba rigunanku ba.Ku juyo ga Ubangiji Allahnku,gama shi mai alheri ne mai tausayi kumamai jinkirin fushi da yawan ƙauna,yakan kuma janye daga aika da bala’i.14Wa ya sani? Ko zai juya yă kuma ji tausayiyă sa mana albarkata wurin hadaya ta gari da hadaya ta shawa Ubangiji Allahnku.
15A busa ƙaho a Sihiyona,a yi shelar azumi mai tsarki,a kira tsarkakan taro.16A tattara mutane;ku tsarkake taron;ku kawo dattawa wuri ɗaya;ku kuma tara yara,da waɗanda suke shan mama.Bari ango yă bar ɗakinsaamarya kuma lolokinta.17Bari firistocin da suke yin hidima a gaban Ubangiji,su yi kuka tsakanin filin haikali da bagade.Bari su ce, “Ka cece mutanenka, ya Ubangiji.Kada ka bar gādonka yă zama abin dariya,da abin ba’a a cikin al’ummai.Me zai sa a ce a cikin mutane, ‘Ina Allahnsu yake?’ ”

Amsar Ubangiji

18Ta haka Ubangiji zai yi kishin ƙasarsayă kuma ji tausayin mutanensa.19Ubangiji zai amsamusu ya ce,“Ina aika da hatsi, sabon ruwan inabi, da mai,isashe da zai ƙosar da ku sosai;ba kuma zan ƙara maishe kuabin dariya ga al’ummai ba.
20“Zan kori sojojin arewa nesa da ku,in tura su cikin busasshiyar ƙasa marar amfani kuma,kuma da sawunsu na gaba zan tura su zuwa gabashin tekuda kuma sawunsu na baya tura su zuwa yammanci a Bahar Rum.Warinsu kuma zai bazu;ɗoyinsu zai tashi.”Tabbatacce ya yi al’amura masu girma.21Kada ki ji tsoro, ya ƙasa;ki yi murna ki kuma yi farin ciki.Tabbatacce Ubangiji ya yi abubuwa masu girma.22Kada ku ji tsoro, ya ku namun jeji,gama wuraren kiwo sun yi kore shar.Itatuwa suna ba da ’ya’yansu;itacen ɓaure da na inabi suna ba da amfaninsu.23Ku yi murna, ya ku mutanen Sihiyona,ku yi farin ciki cikin Ubangiji Allahnku,gama ya ba kuruwan bazara cikin adalci.Yakan aika muku yayyafi a yalwace,na bazara da na kaka, kamar dā.24Masussukai za su cika da hatsi;randuna za su cika da sabon ruwan inabi da mai suna zuba.
25“Zan mayar muku da abin da fāra suka ci a waɗannan shekaruwaɗanda ɗango da fāra masu gaigayewa,da kuma sauran fāra da tarin fārababban mayaƙan da na aika don su fāɗa muku.26Za ku sami a wadace ku ci, har sai kun ƙoshi,za ku kuma yabi sunan Ubangiji Allahnku,wanda ya yi muku ayyukan banmamaki;mutanena ba za su ƙara shan kunya ba.27Sa’an nan za ku sani ina cikin Isra’ila,cewa ni ne Ubangiji Allahnku,babu wani kuma;mutanena ba za su ƙara shan kunya ba.

Ranar Ubangiji

28“Daga baya kuma,zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane.’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci,tsofaffinku za su yi mafarkai,matasanku za su ga wahayoyi.29Har ma a bisan bayina, maza da mata,zan zuba Ruhuna a kwanakin nan.30Zan nuna abubuwan banmamaki a cikin sammaida kuma a kan duniya,za a ga jini da wuta da murtukewar hayaƙi.31Rana za tă duhuntawata kuma yă zama jinikafin isowar babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji.32Amma dukan waɗanda suka nemiUbangiji za su tsira.Kamar yadda Ubangiji ya ce,gama a Dutsen Sihiyona da Urushalimaakwai ceto,a cikin waɗannan da Ubangiji ya kira.