Yowel1hau_bib

1Maganar Ubangiji wadda ta zo wurin Yowel ɗan Fetuwel.

Mamayar da fāra ta yi

2Ku ji wannan, ku dattawa,ku kasa kunne, dukan waɗanda suke zaune a ƙasar.Ko wani abu makamancin haka ya taɓa faruwa a kwanakinkuko a kwanakin kakanninku?3Ku faɗa wa ’ya’yanku,bari kuma ’ya’yanku su faɗa wa ’ya’yansu,’ya’yansu kuma su faɗa wa tsara ta gaba.4Abin da ɗango ya barifāri masu girma sun cinye;abin da fāri masu girma suka bari,burduduwa ta cinye;abin da burduduwa ta bari sauran kwari sun cinye.
5Ku farka, ku bugaggu, ku yi kuka!Ku yi kuka da ƙarfi, ku dukan mashayan ruwan inabi;ku yi kuka mai ƙarfi saboda sabon ruwan inabi,gama an riga an ƙwace ta daga leɓunanku.6Wata al’umma ta mamaye ƙasata,tana da ƙarfi ba ta kuma ƙidayuwa;tana da haƙoran zaki,da zagar zakanya.7Ta mayar da kuringar inabina kangota kuma lalatar da itatuwan ɓaurena.Ta ɓamɓare bayansu dukata kuma jefar da suta bar rassansu fari fat.
8Ku yi makoki kamar budurwaa cikin tsummokitana baƙin ciki domin mijinta na ƙuruciyarta.9Hadayun hatsi da hadayun shaan yanke su daga gidan Ubangiji.Firistoci suna makoki,su waɗanda suke yi wa Ubangiji hidima.10Filaye sun zama marasa amfani,ƙasa ta bushe;an lalatar da hatsi,sabon ruwan inabin ya bushe,mai kuma ba amfani.
11Ku fid da zuciya, ku manoma,ku yi ihu, ku masu noma inabi;ku yi baƙin ciki saboda alkama da sha’ir,saboda an lalata girbin filaye.12Kuringar inabin ta busheitacen ɓaure kuma ya yi yaushi,’ya’yan rumman, itacen dabino da itacen gawasa,dukan itatuwan filaye, sun bushe.Tabbatacce farin cikin ’yan adamya bushe.

Kira don makoki

13Ku sa tsummoki, ya firistoci, ku yi makoki;ku yi ihu, ku da kuke yin hidima a gaban bagade.Zo, ku kwana saye da tsummoki,ku waɗanda kuke yi wa Allahna hidima,gama an yanke hadayun hatsi da hadayun shadaga gidan Allahnku.14Ku yi shelar azumi mai tsarki;ku kira tsarkakan taro.Ku kira dattawada kuma dukan mazaunan ƙasarzuwa gidan Ubangiji Allahnku,ku kuma yi kuka ga Ubangiji.
15Kaito saboda wannan rana!Gama ranar Ubangiji ta kusa,za tă zo kamar hallaka daga wurin Maɗaukaki.
16Ba a yanke abincia idanunmu,farin ciki da kuma murnadaga gidan Allahnmu ba?17Iri suna ta yanƙwanewaa busasshiyar ƙasaƊakunan ajiya sun lalace,an rurrushe rumbunan hatsin,gama hatsi ya ƙare.18Ji yadda dabbobi suke nishi!Garkunan shanu sun ruɗesaboda ba su da ciyawa,har garkunan tumaki ma suna shan wahala.
19A gare ka, ya Ubangiji, nake kira,gama wuta ta cinye wurin kiwoharshen wuta kuma ya ƙone dukan itatuwan jeji.20Har ma namun jeji suna haki gare ka;rafuffuka sun bushewuta kuma ta cinye wurin kiwo a jeji.