1Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,2“Mulki na Allah ne, dole a ji tsoronsa;yana tafiyar da kome yadda ya kamata a cikin sama.3Za a iya ƙirga rundunarsa?A kan wane ne ba ya haska haskensa?4Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki?5In har wata da taurariba su da tsarki a idanunsa,6mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai.Me mutum ya daɗa a gaban Allah!”