Ayuba18hau_bib

Bildad

1Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,2“Yaushe za ka gama maganganun nan?Ka dawo da hankalinka sa’an nan za mu iya yin magana.3Don me muke kamar shanu a wurinka,ka ɗauke mu mutanen wofi?4Kai da ka yayyage kanka don haushi,za a yashe duniya saboda kai ne?Ko kuma duwatsu za su matsa daga wurinsu?
5“An kashe fitilar mugu;harshen wutarsa ya daina ci.6Wutar cikin tentinsa ta zama duhu;fitilar da take kusa da shi ta mutu.7Ƙarfin takawarsa ya ragu;dabararsa ta ja fāɗuwarsa.8Ƙafafunsa sun kai shi cikin raga,yana ta yawo a cikin ragar.9Tarko ya kama ɗiɗɗigensa;tarko ya riƙe shi kam.10An ɓoye masa igiya da za tă zarge shi a ƙasa;an sa masa tarko a kan hanyar da zai bi.11Tsoro duk ya kewaye shi ta kowane gefeyana bin shi duk inda ya je.12Masifa tana jiransa;bala’i yana shirye yă fāɗa masa a lokacin da zai fāɗi.13Ya cinye wani sashe na gaɓar jikinsa;ɗan fari na mutuwa ya cinye ƙafafunsa.14An yage shi daga zaman lafiyar da yake yi a cikin tentinsaaka sa shi tsoro sosai.15Wuta ta cinye tentinsa;farar wuta ta rufe wurin da yake zama.16Jijiyoyinsa sun bushe a ƙasarassansa sun mutu a sama.17An manta da shi a duniya;ba wanda yake ƙara tunawa da shi.18An tura shi daga cikin haske zuwa cikin duhu,an kore shi daga duniya.19Ba shi da ’ya’ya ko zuriya cikin mutanensa,ba sauran wanda yake a raye a wurin da ya taɓa zama.20Mutanen Yamma suna mamakin abin da ya faru da shi;tsoro ya kama mutanen gabas.21Ba shakka haka wurin zaman mugun mutum yake,haka wurin zaman wanda bai san Allah ba yake.”