Ayuba16hau_bib

Ayuba

1Sai Ayuba ya amsa,2“Na ji abubuwa da yawa kamar waɗannan;dukanku ba ku iya ta’aziyya ba!3Dogayen surutanku ba sa ƙare ne?Me yake sa kuke ta yin waɗannan surutai har kuke cin gaba da yin gardama?4Ni ma zan iya yin maganganu kamar yadda kuke yiin da kuna cikin halin da nake;zan iya faɗar duk abubuwan da kuke faɗi,in kaɗa muku kaina.5Amma bakina zai ƙarfafa ku;ta’aziyyar da za tă fito daga bakina za tă kawar muku da ɓacin zuciyarku.
6“Duk da haka in na yi magana, ba na samun sauƙi;in ma na yi shiru zafin ba ya tafiya.7Ba shakka ya Allah ka gajiyar da ni;ka ɓata gidana gaba ɗaya.8Ka daure ni, ya kuma zama shaida;yadda na rame sai ƙasusuwa, wannan ya sa ake gani kamar don ni mai zunubi ne shi ya sa.9Allah ya kai mini hari ya yi kaca-kaca da ni cikin fushinsayana cizon haƙoransa don fushin da yake yi da ni;ya zura mini ido.10Mutane suka buɗe baki suka yi mini riyar reni;suka yi mini ba’asuka haɗu suka tayar mini.11Allah ya bashe ni ga mugayen mutane,ya jefa ni hannun mugaye.12Dā ina zamana lafiya kome yana tafiya daidai;amma ya ragargaza ni; ya shaƙe ni a wuya;ya murƙushe ni na zama abin barata gare shi;13maharbansa sun kewaye ni.Ba tausayi, ya soke ni a ƙodatahar jini ya zuba a ƙasa.14Ya ji mini rauni a kai a kaiya auko mini kamar mai yaƙi.
15“Ina makoki saye da tsummokina ɓoye fuskata a cikin ƙura.16Fuskata ta yi ja don kukaidanuna sun kukumbura;17duk da haka hannuwana ba su aikata ɓarna bakuma addu’ata mai tsabta ce.
18“Ya duniya, kada ki ɓoye jinina;bari yă yi kuka a madadina!19Ko yanzu haka shaidata tana sama;wanda zai tsaya mini yana sama.20Shi mai yin roƙo a madadina abokina neyayinda nake kuka ga Allah;21a madadin mutum ya yi roƙo ga Allahkamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.
22“Shekaru kaɗan suka ragein kama hanyar da ba a komawa.