Irmiya50hau_bib

Saƙo game da Babilon

1Ga maganar Ubangiji da ya yi ta wurin Irmiya annabi game da Babilon da kuma ƙasar Babiloniyawa.2“Ka yi shela ka kuma furta a cikin al’ummai,ka tā da tuta ka kuma furta;kada ku ɓoye kome, amma ku ce,‘Za a ci Babilon da yaƙi;za a kunyata Bel,Marduk ya cika da tsoro.Siffofinta za su sha kunyagumakanta za su cika da tsoro.’3Al’umma daga arewa za tă fāɗa matasu mai da ƙasar kango.Ba wanda zai zauna a cikinta;mutane da dabbobi za su gudu.
4“A kwanakin nan, a wannan lokaci,”in ji Ubangiji,“mutanen Isra’ila da mutanen Yahuda gaba ɗayaza su tafi cikin hawaye su nemi Ubangiji Allahnsu.5Za su tambayi hanyar zuwa Sihiyonasu kuma juya fuskokinsu wajenta.Za su zo su haɗa kansu ga Ubangijia madawwamin alkawarida ba za a manta da shi ba.
6“Mutanena sun zama ɓatattun tumaki;makiyayansu sun bauɗar da susuka sa suna ta yawo a cikin duwatsu.Sun yi ta yawo a bisa dutse da tudusuka manta wurin hutunsu.7Duk wanda ya same su ya cinye su;abokan gābansu suka ce, ‘Ba mu da laifi,gama sun yi zunubi wa Ubangiji, wurin kiwonsu na gaske,Ubangiji, abin sa zuciyar kakanninsu.’
8“Ku gudu daga Babilon;ku bar ƙasar Babiloniyawa,ku zama kamar awakin da suke bi da garke.9Gama zan kuta in kuma kawo a kan Babilonhaɗinkan manyan al’ummai na arewa.Za su ja dāgār gāba da ita,kuma daga arewa za a ci ta da yaƙi.Kibiyoyinsu za su zama kamar na gwanayen jarumawawaɗanda ba sa dawowa hannu wofi.10Saboda haka za a washe Babiloniyawa;dukan waɗanda suka washe ta za su ƙoshi,”in ji Ubangiji.
11“Saboda kuna farin ciki kuna kuma murna,ku da kuka washe gādona,domin kuna tsalle kamar karsana mai sussuka hatsikuna kuma haniniya kamar ingarmu.12Mahaifiyarku za tă sha babbar kunya;ita da ta haife ku za tă sha kunya.Za tă zama mafi ƙanƙanta na al’ummai,jeji, busasshiyar ƙasa, hamada.13Saboda fushin Ubangiji ba za tă zauna a cikinta baamma za tă zama kufai gaba ɗaya.Duk waɗanda suka wuce Babilon za su ji tsoro su kuma yi tsakisaboda dukan mikinta.
14“Ku ja dāgā kewaye da Babilon,dukanku waɗanda kuke jan baka.Ku harbe ta! Kada ku rage kibiyoyi,gama ta yi zunubi ga Ubangiji.15Ku yi kuwwa a kanta a kowane gefe!Ta miƙa wuya, hasumiyarta ta fāɗi,katangarta sun rushe.Da yake wannan sakayya ce ta Ubangiji,ku ɗauki fansa a kanta;yi mata yadda ta yi wa waɗansu.16Ku datse wa Babilon mai shuka,da mai girbi lauje a lokacin girbi.Saboda takobin mai zaluncibari kowa ya koma ga mutanensa,bari kowa ya gudu zuwa ga ƙasarsa.
17“Isra’ila garke ne da ya watseda zakoki suka kora.Na farkon da ya cinye shisarkin Assuriya ne;na ƙarshen da ya ragargaza ƙasusuwansaNebukadnezzar sarkin Babilon ne.”18Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa,“Zan hukunta sarkin Babilon da ƙasarsayadda na hukunta sarkin Assuriya.19Amma zan komo da Isra’ila zuwa wurin kiwonsazai kuwa yi kiwo a Karmel da Bashan;zai ƙosar da marmarinsaa tuddan Efraim da Gileyad.20A kwanakin nan, da kuma a lokacin nan,”in ji Ubangiji,“za a yi bincike don laifin Isra’ila,amma ba za a samu ba,kuma don zunubin Yahuda,amma ba za a sami wani abu ba,gama zan gafarta wa raguwar da na rage.
21“Ku fāɗa wa ƙasar Meratayimda waɗanda suke zama a Fekod.Ku fafara, ku kashe kuma hallaka su sarai,”in ji Ubangiji.“Ku aikata dukan abin da na umarce ku.22Hargowar yaƙi tana a ƙasar,hargowar babbar hallaka!23Dubi yadda aka karya aka kuma ragargazagudumar dukan duniya!Dubi yadda Babilon ta zama kufaia cikin al’ummai!24Na sa miki tarko, Babilon,kika kuwa kamu kafin ki sani;aka same ki aka kuma kama kidomin kin tayar wa Ubangiji.25Ubangiji ya buɗe taskar makamansaya fitar da makaman fushinsa,gama Maɗaukaki Ubangiji Mai Iko Duka yana da aikin da zai yia ƙasar Babiloniyawa.26Ku zo ku yi gāba da ita daga nesa.Ku buɗe rumbunanta;ku jibga ta kamar tsibin hatsi.Ku hallaka ta saraikada ku bar mata raguwa.27Ku kashe dukan ’yan bijimantabari su gangara zuwa mayanka!Kaitonsu! Gama ranansu ta zo,lokaci ya yi da za a hukunta su.28Ku saurari masu gudun hijira da masu neman mafaka daga Babilonsuna furtawa a Sihiyonayadda Ubangiji Allahnmu ya ɗauki fansa,fansa domin haikalinsa.
29“Ku kira ’yan baka a kan Babilon,dukan waɗanda suke jan baka.Ku yi sansani kewaye da ita duka;kada ku bar wani ya tsira.Ku sāka mata don ayyukanta;ku yi mata yadda ta yi.Gama ta tayar wa Ubangiji,Mai Tsarkin nan na Isra’ila.30Saboda haka, samarinta za su fāɗi a tituna;za a kawar da dukan sojojinta a wannan rana,”in ji Ubangiji.31“Ga shi, ina gāba da ke, ya ke mai girman kai,”in ji Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki,“gama ranarki ta zo,lokacin da za a hukunta ki.32Mai ɗaga kai za tă yi tuntuɓe ta kuma fāɗikuma ba wanda zai taimake ta tă tashi;zan hura wuta a garuruwantada za tă cinye duk waɗanda suke kewaye da ita.”33Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,“An danne mutanen Isra’ila, haka ma mutanen Yahuda.Dukan waɗanda suka kama su suna riƙe su kankan,suna kin barinsu su tafi.34Duk da haka Mai Fansarsu yana da ƙarfi;Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.Zai kāre muradunsu gabagadidon yă kawo hutu ga ƙasarsu,amma rashin hutu ga waɗanda suke zaune a Babilon.
35“Akwai takobi a kan Babiloniyawa!”In ji Ubangiji“a kan waɗanda suke zama a Babilonda kuma a kan fadawanta da masu hikimarta!36Akwai takobi a kan annabawan ƙaryanta!Za su zama wawaye.Akwai takobi a kan jarumawanta!Za su cika da tsoro.37Akwai takobi a kan dawakanta da kekunan yaƙintada kuma dukan baƙin da suke cikin mayaƙanta!Za su zama mata.Akwai takobi a kan dukiyarta!Za a washe su.38Fări a kan ruwanta!Za su bushe ƙaf.Gama ƙasa ce ta gumaka,gumakan da za su haukace da tsoro.
39“Saboda haka halittun hamada da kuraye za su zauna a can,a can kuma mujiya za tă zauna.Ba za a ƙara zaunako a yi zama a cikinta ba daga tsara zuwa tsara.40Yadda Allah ya tumɓuke Sodom da Gomorratare da maƙwabtan garuruwansu,”in ji Ubangiji“haka ma ba wanda zai zauna a can;ba wani da zai zauna a cikinta.
41“Duba! Ga sojoji suna zuwa daga arewa;babbar al’umma da sarakuna masu yawasuna tahowa daga iyakokin duniya.42Suna riƙe da baka da māshi;mugaye ne marasa tausayi.Amonsu ya yi kamar rurin tekuyayinda suke hawan dawakansu;suna zuwa kamar mutane a dāgār yaƙidon su fāɗa miki, ya Diyar Babilon.43Sarkin Babilon ya ji rahotanni game da su,hannunsa kuma ya yi laƙwas.Wahala ta kama shi,zafi kamar na mace mai naƙuda.44Kamar zaki mai haurawa daga kurmin Urdunzuwa wurin kiwo mai dausayi,zan fafare Babilon daga ƙasan nan da nan.Wane ne zaɓaɓɓen da zan naɗa domin wannan?Wane ne kamar ni da zai kalubalance ni?Kuma wanda makiyayi zai iya tsaya gāba da ni?”
45Saboda haka, ku ji abin da Ubangiji ya shirya a kan Babilon,abin da ya nufa gāba da ƙasar Babiloniyawa.Za a kwashe ƙananan garkensu a tafi;zai hallaka wurin kiwonsu sarai saboda su.46Da jin an ci Babilon da yaƙi sai duniya ta girgiza;za a ji kukanta cikin al’ummai.