Irmiya4hau_bib
1“In za ka komo, ya Isra’ila,ka komo gare ni,”in ji Ubangiji.“In ka kau da gumakanka masu banƙyama daga gabanaba ka ƙara karkace ba,2kuma in cikin gaskiya da adalcika rantse, ‘Muddin Ubangiji yana raye,’to al’ummai za su sami albarka ta wurinsakuma a cikinsa za su ɗaukaka.”3Ga abin da Ubangiji yana ce wa mutanen Yahuda da kuma na Urushalima.“Ku nome ƙasarkukuma kada ku yi shuka cikin ƙayayyuwa.4Ku yi wa kanku kaciya ga Ubangijiku yi wa zukatanku kaciya,ku mutanen Yahuda da mutanen Urushalima,in ba haka ba hasalata za tă sauko ta ci kamar wutasaboda muguntar da kuka aikataza tă ci ba wanda zai kashe ta.