1Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga Ubangiji.2“Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ka rubuta a cikin littafi dukan maganganun da na yi maka.3Kwanaki suna zuwa,’ in ji Ubangiji, ‘sa’ad da zan komo da mutanena Isra’ila da Yahuda daga bauta in kuma maido da su ga ƙasar da na ba wa kakanninsu mallaka,’ in ji Ubangiji.”4Ga kalmomin Ubangiji da ya yi game da Isra’ila da Yahuda,5“Ga abin da Ubangiji yana cewa,“ ‘Ana jin kukan tsoro,razana, ba salama ba.6Ku tambaya ku ji.Namiji zai iya haifi ’ya’ya?To, me ya sa kuke ganin kowane mai ƙarfida hannuwansa a kwankwaso kamar mace mai naƙuda,kowace fuska ta koma fari?7Kaito, gama wannan rana za tă zama mai girma!Babu kamar ta.Zai zama lokacin wahala wa Yaƙub,amma za a cece shi daga cikinta.8“ ‘A wannan rana,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki,‘Zan karya karkiya daga wuyansuzan kuma cire musu kangi;baƙi ba za su ƙara bautar da su ba.9A maimakon haka, za su bauta wa Ubangiji AllahnsuDawuda sarkinsu kuwa,wanda na tayar musu.10“ ‘Saboda haka kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana;kada ka karai, ya Isra’ila,’in ji Ubangiji.‘Tabbatacce zan cece ka daga wuri mai nesa,zuriyarka daga ƙasar zaman bautansu.Yaƙub zai sami salama da zaman lafiya,kuma ba wanda zai sa ya ji tsoro.11Ina tare da kai zan kuma cece ka,’in ji Ubangiji.‘Ko da yake na hallakar da dukan al’umma gaba ɗayaa inda na warwatsa ku,ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba.Zan hore ku amma da adalci kaɗai;ba zan ƙyale ku ku tafi gaba ɗaya ba hukunci ba.’12“Ga abin da Ubangiji yana cewa,“ ‘Mikinku marar warkewa ne,raunin da kuka ji ya sha ƙarfin warkarwa.13Babu wanda zai yi roƙo saboda damuwarku,ba magani domin mikinkubabu warkarwa dominku.14Dukan abokanku sun manta da ku;ba su ƙara kulawa da ku.Na buge ku kamar yadda abokin gāba zai yina kuma hukunta ku yadda mai mugunta zai yi,domin laifinku da girma yakezunubanku kuma da yawa suke.15Me ya sa kuke kuka a kan mikinku,wahalarku da ba ta da magani?Domin laifinku da girma yake da kuma zunubanku masu yawana yi muku waɗannan abubuwa.16“ ‘Amma duk wanda ya cinye ku za a cinye shi;dukan abokan gābanku za su tafi zaman bauta.Waɗanda suka washe ku su ma za a washe su;dukan waɗanda suka mai da ku ganima su ma zan mai da su ganima.17Amma zan mayar muku da lafiyain kuma warkar da mikinku,’ in ji Ubangiji,‘domin ana ce da ku yasassu,Sihiyona wadda ba wanda ya kula da ita.’18“Ga abin da Ubangiji yana cewa,“ ‘Zan mayar da wadatar tentin Yaƙubin kuma ji tausayin wuraren zamansa;za a sāke gina birnin a kufansa,fadar kuwa za tă tsaya a wurin da ya dace da ita.19Daga gare su waƙoƙi za su fito na godiyada kuma sowa ta farin ciki.Zan riɓaɓɓanya su,ba za su kuwa ragu ba;zan kawo musu ɗaukaka,ba kuwa za a ƙasƙanta su ba.20’Ya’yansu za su kasance kamar a kwanakin dājama’arsu kuma za su kahu a gabana;zan hukunta duk wanda ya zalunce su.21Shugabansu zai zama ɗaya daga cikinsu;mai mulkinsu zai taso daga cikinsu.Zan kawo shi kusa zai kuma zo kusa da ni,gama wane ne zai miƙa kansadon yă yi kusa da ni?’In ji Ubangiji.22‘Saboda haka za ku zama mutanena,ni kuwa in zama Allahnku.’ ”23Ga shi, hadarin Ubangijizai fasu cikin hasala,iskar guguwa mai hurawaa kan kawunan mugaye.24Fushi mai zafi na Ubangiji ba zai kawu basai ya cikamanufofin zuciyarsa gaba ɗaya.A kwanaki masu zuwaza ku gane wannan.